<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>187</hymn_number>
<title>Na Sami Ceto Ta Wurin Yesu LW187</title>
<lyrics>[V1]
 1) Na sami ceto ta wurin Yesu.
 Shi ne Ɗan Ragon da Allah ya bayar
 Domin ya mutu saboda mu,
 Mu sami pansarmu wurinsa.

[V2]
 KORUS
 Ceto na Allah kyauta ne
 Ceto na Allah kyauta ne.
 Yesu Mai Ceto,
 Alhamdu ga Allah,
 I, Ceto na Allah kyauta ne.

[V3]
 2) Na yi ƙoƙari in sami ceto
 Cikin ayyukan da jiki ke yi,
 Ni dai na kasa, duk banza ne.
 Ai, ceto na Allah kyauta ne.
 Korus

[V4]
 3) Ran da na tuba na sami ceto,
 Yesu ya yafe duk zunubaina,
 Na sami rai na har abada,
 Bukata ta biya, an cece ni.
 Korus

[V5]
 4) Duk ƴanuwana, ku zo wurinsa,
 Yau sai ku tuba, ku karƃi Yesu,
 Bar neman ceto gun ayyuka
 Don ceto na Allah kyauta ne.
 Korus</lyrics>
</song>